Ma'aikatan jiragen sama zasu yi taro a Abuja

Hatsarin jirgi a Najeriya
Image caption Mutane da dama sun rasa rayukansu a hadarin jirgi

A Najeriya, kungiyoyin ma'aikatan jiragen sama sun kira wani taro a Abuja babban birnin Kasar domin duba halin da sha'anin zirga-zirgar jiragen sama ya shiga a kasar.

Kungiyoyin wadanda suka hada da ta matuka jiragen sama, da ta Injiyoyin jiragen da kuma ta ma'aikatan filayen sauka da tashin jiragen saman sun ce suna son lalubo hanyoyin da za a bi domin magance yawaitar hadurran jiragen sama a kasar.

Kungiyoyin dai sun ce akwai ban tsoro ga yadda ake yawan samun matsalar a fannin na sufurin jiragen sama.

Ko a farkon watan Oktobar da ake ciki sai da wani jirgin sama yai hatsari jim kadan bayan tashin sa daga Lagos abinda yai sanadiyyar mutuwar mutane akalla goma sha shida.

Karin bayani