'Yan Najeriya miliyan 56 basu iya rubutu ba

Image caption Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan

Hukumar yaki da jahilci a Najeriya ta ce kashi 35 cikin 100 na 'yan kasar basu iya rubuta da karatu ba.

A cewar hukumar alkaluman sun nuna cewar mutane miliyan 56 a Najeriya basu iya rubuta da karatu ba.

Shugaban hukumar, Malam Jibrin Yusuf Paiko a hirarsa da BBC ya ce dole ne sai gwamnatoci a matakai daban-daban sun zage damtse wajen ganin an rage yawan masu fama da jahilci a Najeriya.

Hukumar ta ce jihohin da basa wayar da kan jama'a wajen yaki da jahilci sune suka fi samun koma baya wajen yawan mutanen da basu iya rubutu da karatu ba.

Karin bayani