PDP ta maida martani ga 'yan sabuwar PDP

Jam'iyyar PDP
Image caption Gwamnonin sabuwar PDP sunyi barazanar ficewa daga PDP

A Najeriya, jam'iyyar PDP mai mulkin Kasar ta bayyana shirin sauya-shekar da 'yan sabuwar PDP ke yi da cewar barazana ce kawai.

Barista Abdullahi Jallo shine mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar PDP kuma ya shaidawa BBC cewa magana suke kawai ta cikin fushi amma ya ce ana nan ana sasantawa.

Jam'iyyar na maida martani ga wani zabi da 'yan sabuwar PDPn suka ce su na dubawa bayan wani taron da suka yi, na shiga jam'iyyar adawa ta APC ko kuma su kafa wata.

Kusan watanni uku kenan da ballewar 'yan sabuwar PDP sakamakon zargin da suke yi cewa ana kama-karya a cikin jam'iyyar, kana suka bukaci a sauke Alhaji Bamanga Tukur daga shugabancin jam'iyyar.

Karin bayani