Spain na zargin Amurka da leken asiri

Image caption Spain na shirn nuna yatsa ga Amurka kan leken asiri

Kafofin yada labarai na kasar Spain sun ba da rahoton cewa hukumar tsaron kasa ta Amurka cikin sirri ta rinka sauraren layukan waya na mutane miliyan 60 a cikin wata guda kacal.

Rahotannin suka ce an samu cikakken bayanin sauraren wayoyin mutanen da aka rinka yi ne a cikin watan Disamba daga takardun bayanan sirri da tsohon jami'in leken asirin nan na Amurkar Edward Snowden ya tsegunta.

Kafofin yada labaran na Spain suka ce bayanan da hukumar tsaron kasar ta Amurka ta nada sun hada da lambobi da wuraren da wadanda suka bugo wayar suke da kuma wadanda suka amsa wayoyin, kodayake ba a ambaci bayanin maganganun da suka yi ba.

An nemi jakadan Amurka a kasar ta Spain ya kai kansa ma'aikatar harkokin wajen Spain a yau Litinin don tattaunawa da shi a kan zargin farko da aka yi na leken asirin da gwamnatin Amurka ta rinka yi wa 'yan siyasa da jama'ar kasar ta Spain.

Karin bayani