Wikipedia na tura sakonni ta salula

Wikipedia
Image caption Wikipedia

Shafin Wikipedia ya fara wani aikin gwaji na tura sakonnin wayar salula ga masu bukatar shafin a Afrika.

Shafin mai tattara bayanan fannonin ilimi dabam dabam a intanet ya hada kai ne da kamfanin wayar salula na Airtel domin samar da bayanan kyauta a wani gwaji da ya ke gudanarwa a Kenya.

Ana fatan shirin zai bai wa wadanda basu da halin shiga intanet damar amfani da shafin na Wikipedia.

Manajan fasaha na giduniyar Wikimedia, Dan Foy ya ce za'a gudanar da gwajin ne tsawon watanni uku.

Fasahar Salula a Afirka

Amfani da wayar salula mai arha dai ya zama ruwan dare a Afirka kuma harkar wayar salula a nahiyar har ta zarta ta kasashen da suka ci gaba.

Ga misali, aikewa da kudi ta wayar salula ya yi matukar yaduwa - inda fiye da mutane miliyan 17 a kasar Kenya ke aikewa da kudi bisa tsarin M-Pesa.

Kamfanonin fasaha na yammacin duniya na kallon Afirka a matsayin wata nahiya da za su iya bunkasa harkokinsu. Alal misali Facebook, na kokarin habaka karbuwarsa a nahiyar Afirka bayanda ya yi kaka-gida a kasashen da suka cigaba.

Editan shafin intanet kan fasaha a Afrika HumanIPO, Tom Jackson ya ce shirin na Wikipedia na da matukar fa'ida.

Yace; "Ana samun karuwar sanya bayanai na ilimi daga kasahen Afirka da dama a shafukan intanet, sai dai rashin wadatar intanet din na kawo cikas kasancewar mafi yawan 'yan Afirka na amfani da wayoyin salula ne wurin shiga intanet."

"Wannan shirin zai taimaka wurin baiwa wadanda ba su da intanet damar amfani da dimbin ilimin da aka tara a shafin Wikipedia."

"Sai dai ina fatan sakon wayar salular zai hada da gargadin cewa batutuwan da ke cikin Wikipedia ba su da tabbas kamar dai yadda ake gargadin yaran nahiyar Turai da Amurka da su ke amfani da intanet."