A sauya wa sojoji makamansu - Geidam

Image caption Gwamna Geidam ya ce makaman sojoji basu da inganci

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta sauya makaman da jami'an tsaro suke amfani da su wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

A cewar gwamnan, makaman da 'yan kungiyar ke amfani da su sun fi na jami'an tsaro inganci.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ziyararsa wurin da 'yan Boko Haram su ka kai hari inda mutane da dama suka hallaka.

Wasu majiyoyi na asibitin Damaturu, sun ce a karshen mako an kai gawawakin mutane kusan 35 wasunsu sanye da kayan sarki.

Jihar Yobe na daga cikin jihohi ukun da Shugaba Jonathan ya kafa dokar ta baci a kokarin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Karin bayani