'Yan bindiga sun sace dala miliyan 54 a Libya

Image caption 'Yan bindiga a Libya

Kamfanin Dillancin labaran kasar Libya-Lana,ya ce wasu 'yan bindiga sun sace kusan dala miliyan 54 a wani hari da suka kai wa motar da ke dauke da kudaden kasashe daban-daban da za a kai babban bankin kasar ta Libya.

'Yan bindigar su goma dauke da muggan makamai sun tare motar ne a hanyar birnin Sirte na kasar.

Kamfanin dillancin labaran ya ce motar na tahowa ne daga filin jirgin sama da ke babban birnin kasar Tripoli, dauke da kudaden da za a rabawa rassan babban bankin kasar.

An ambato wani jami'in tsaro a Sirte na cewa an gano motar da aka yi amfani da ita wajen yin satar kuma 'yan sanda na farautar wadanda suka aikata satar.

Kasar Libya na fuskantar rashin tabbas tun bayan hambarar da Shugaba Muammar Gaddafi a shekara ta 2011.

Karin bayani