Faransa ta jinjinawa mahukuntan Nijar

Kamfanin  Areva a Niger
Image caption Kamfanin Areva a Niger

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya ce an sako 'yan kasar Faransar su hudu wadanda wasu 'yan gwagwarmaya suka sace a Niger sama da shekaru uku da suka gabata.

Ya ce ministan harkokin waje, da kuma na tsaron Faransa zasu tafi kasar ta Nijar, kuma ba tare da bata lokaci ba mutanen da aka sako zasu koma Faransa.

Kungiyar Al Qaeda a yankin Maghreb ne suka sace su a garin Arlit mai arzikin uranium, inda suke aiki da kampanin makamashin nukiliyar Faransa na Areva.

Wadanda suka sace su , sun bukaci a biya dala miliyan dari da talatin a matsayin kudaden fansa.

Ministan harkokin wajen Faransar, Laurent Fabius ya ce mutanen na cikin koshin lafiya, kuma babu wasu kudaden fansa da aka biya.