Hargitsi a jihar Edo kan taron kasa

Image caption Gwamna Adams Oshiomole

An samu hargitsi a jihar Edo a wajen sauraron ra'ayoyin jama'a da kwamitin neman shawarwari kan shirya babban taro na kasa ya shirya a Benin babban birnin Jihar.

An fara rikicin ne lokacin da gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya ke jawabi inda yake cewa "taron bashi da amfani domin za a kashe kudin al'umma ne kawai ba tare da an cimma wani abu mai ma'ana ba".

Kalaman gwamna Oshiomole bai yiwa wasu dadi ba, inda daya daga cikin 'yan kwamitin, Kanar Tony Nyiam mai ritaya ya katse maganar Oshiomole, saboda rashin amincewa da jawabin gwamnan.

Hakan ne ya janyo hargitsi inda matasa, wadanda gwamnatin Jihar Edo ta bayyana a matsayin 'yan bangar siyasa suka soma ihu cikin zauren, abinda yasa mukarraban gwamnan Oshiomole suka rufa masa baya, ya fice daga zauren.

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan kwamitin da shugaban kasa ya nada, sun bukaci Kanar Tony Nyiam ya yi murabus daga cikin kwamitin saboda wannan rikicin daya faru a jihar ta Edo.