Fararen hula na tserewa daga Damascus

Syria
Image caption Syria

Dubunnan fararen hula na tserewa daga wata unguwar birnin Damascus a Syria bayanda dakarun gwamnati su ka sassauta kawanyar da suka yi mata.

Wakilin BBC a Damascus ya ce galabaitattun mutane ne ke tserewa daga unguwar Moadamiyah, wacce ke shan luguden bama-bamai tun cikin watan Maris.

Unguwar ta na fama da karancin abinci da ruwan sha da kuma kayan masarufi.

A baya dai, rundunar sojin Syria ta ce ko dai yankunan Damascus da ke karkashin ikon 'yan tawaye su mika wuya ko kuma yunwa ta hallakasu.

A farkon watan nan ne wani malamin Islama ya bada fatawar da ta halattawa mazauna yankunan cin naman karnuka da maguna domin tsira da ransu.