An kama el-Arian na Kungiyar 'yan uwa musulmi

Janar Abdel Fattah al -Sisi
Image caption Ana tsare da Mr el-Arian a birnin alkahira.

Kafar yada labaran Masar ta ce an kama wani babban dan siyasa Essam el-Arian

Essam el-Arian dai ya kasance babban mamba a kungiyar 'yan uwa musulmi kuma mataimakin shugaban jam'iyyar Justice and Freedom.

Ana tsare da Mr el-Arian a birnin alkahira.

Masu shigar da kara a Masar sun bada damar kama Essam el-Arian tun a watan Yulin wannan shekarar,bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Muhammad Morsi wanda ya kasance shi ma dan jam'iyyar Justice and Freedom.

Karin bayani