Gwarzon Forbes: Dangote da Ovia na takara

Image caption Alhaji Aliko Dangote

Mujallar Forbes ta sanarda sunayen mutane biyar, wanda a cikinsu za ta zabi gwarzon shekara ta 2013.

A watan Disamba a wani buki da za ayi a Nairobi na kasar Kenya za a bada kyautar.

Cikin mutane biyar din da mujallar ya kebe uku 'yan Najeriya ne, sai dan kasar Afrika ta Kudu mutum daya sai kuma daya mutumin dan kasar Zimbabwe.

Mutanen sune;

1. Alhaji Aliko Dangote shine wanda yafi kowanne dan Afrika arziki kuma ya samu dukiyarsa ta hanyar kasuwancin siminti da harkokin man fetur kuma yana amfani da arzikinsa wajen taimakawa miliyoyin jama'a a nahiyar Afrika.

2. Mr Akinwunmi Adesina, ministan ayyukan gona a Najeriya, wanda burinsa shine maida kasar kan hanyar samarda isashen abinci sannan ya yiwa manoma akalla miliyan 20 rijista daga nan zuwa shekara ta 2015.

3. Jim Ovia wanda ya kafa bankin Zenith a Najeriya a shekarar 1990 kuma a yanzu bankin shine na biyu mafi karfin jari a yankin yammacin Afrika. A yanzu ya maida hankali ne wajen bunkasa harkokin kasuwanci a Afrika.

4. Dan Afrika ta Kudu, Patrice Motsepe wanda ke harkokin hako ma'adinai a kasar kuma a yanzu yana shirin bada rabin dukiyarsa ga talakawa.

5. Strive Masiyiwa wanda ya kafa kamfanin sadarwa na Econet Wireless a yanzu yana amfani da gidauniyarsa Capernaum wajen ilimantar da dubban marayu a kasar Zimbabwe.

Karin bayani