Hadarin mota ya kashe mutane 40 a India

Hatsarin India
Image caption Hatsarin India

Akalla mutane 40 ne suka mutu bayanda motar da suke tafiya a cikinta ta kama da wuta a kudancin India.

Yan sanda sun ce motar na dauke da mutane 49 daga Bangalore zuwa Hyderabad.

Motar ta yi karo ne da wani ginin raba hanya yayinda mafi yawan fasinjojin ke bacci.

Rahotanni sun ce kofofin motar da ake sarrafasu da mukullin direba sun bame, abinda ya sa fasinjojin suka kasa bude su.

Shi kuma direban da ya fice ta taga ya samu kulawar likitoci inda yanzu kuma ya ke amsa tambayoyi daga 'yan sanda.