Mummunan hadarin jirgin kasa a Kenya

jirgin kasa a kenya
Image caption jirgin kasa a kenya

Akalla mutane 11 ne suka rasu yayinda 34 suka jikkata a Nairobi, babban birnin Kenya lokacinda jirgin kasa ya yi karo da motar bas.

Shugaban 'yan sandan Nairobi Benson Kibui ya ce motar na tsallaka layin dogo lokacin da jirgin ya tunkaro a guje.

Wadanda suka shaida hadarin sun ce matukin jirgin ya tsira da ransa kuma nan take ya karasa cocin God's Last Appeal wanda ke daura da wurin inda ya durkusa domin yin addu'a.

Masu aiko rahotanni sun ce rashin daukar matakan kariya a tituna da digogin jirgin kasa na yawan haddasa hadurra a Kenya.