Majalisar wakilan Nigeria za ta kamo minista

Stella Oduah
Image caption Stella Oduah

Majalisar wakilan Nigeria na barazanar ba da umarnin kama ministar sufurin jiragen sama bayan da ta ki bayyana a gaban kwamitin majalisar.

Kwamitin na binciken Mrs Stella Oduah ne bisa motoci biyu masu sulke da kudinsu ya kai naira miliyan 255 da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar ta sayo domin amfanin ministar.

Majalisar ta ce sayen motocin ya sabawa doka saboda baya cikin tanade-tanaden kasafin kudin Nigeria na bana.

Dan kwamitin Muhammad Ali Wudil ya ce rashin bayyanar ministar, "gadara ce da kuma karan tsaye ga tsarin mulkin Nigeria."

Tuni dai shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya kafa wani kwamiti da zai binciki ministar game da wannan batu.