Hukumar leken asirin Amurka ta kare ayyukanta

James Clapper
Image caption An zargi Amurka da leken asirin kawayen ta

Babban jami'in hukumar leken asirin Amurka ya kare aikace-aikacen hukumar a gaban 'yan majalisar dokokin Kasar.

Shaidar da ya bayar a zaman jin bahasin na zuwa ne bayan yawaitar zarge-zargen cewar hukumar na satar bayanan sirrin abokanta na kasashen Turai da wasu daga cikin 'yan kasar Amurkar.

Daraktan hukumar leken asirin James Clapper ya shaidawa zaman jin bahasin cewa duk wani kuskure da aka samu ajizanci ne na dan Adam.

Shugaban hukumar leken asirin Amurkar Janar Keith Alexander ya ce rahotannin kafafen watsa labarai akan nadar bayanan sirrin mutane a kasashen France, da Italy da Spain ba gaskiya bane.

Wakilin BBC yace jami'an leken asirin dai basu amsa wasu tambayoyi masu zafi ba a zaman jin bahasin, hasali ma duk wanda yake tsammanin shugabannin lekan asirin zasu nemi afuwa ko kuma zasu kunyata a wannan zama, zai sha mamaki.

Karin bayani