Wasu 'yan Abyei sun fi son Sudan ta Kudu

Image caption Sudan da Sudan ta Kudu na takkadama a kan Abyei

Mazauna yankin Abyei da ake takaddama a kai sun kada kuri'a tare da gagarumin rinjaye na su kasance tare da Sudan ta Kudu.

A kuri'ar raba gardama da ba ta hukuma ba wadda daya daga cikin manyan kabilun yankin 2 ce kadai ta shiga cikinta, sakamakon ya nuna cewar.

Kakakin kwamitin shirya kuri'ar raba gardamar a Abyei ya ce kashi 99 cikin 100 na wadanda suka kada kuri'a --daga kabilar Ngok Dinka ne suka amince da bin kasar Sudan ta Kudu.

Wakilan Larabawan Misseriya wadanda kawayen Sudan ne , kuma suka ki shiga cikin kuri'ar raba gardamar sun ce ba za su amince da sakamakon kuri'ar ba.

Kungiyar Tarayyar Afrika ta bayyana kuri'ar raba gardamar a matsayin wata barazana ga zaman lafiya tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

Karin bayani