APC na zawarcin Gwamnonin sabuwar PDP

PDP da APC
Image caption Jam'iyyar APC da PDP na musayar kalamai

A yau ne ake saran manyan shugabannin jam'iyyar hamayya ta APC a Nigeria zasu ci gaba da ziyarar da suke yi ga wasu gwamnonin sabuwar PDP da suka balle daga jam'iyyar.

Ranar Alhamis ne dai shugabannin jam'iyyar ta APC suka ziyarci gwamnonin Kano Rabi'u Musa kwankwaso da na Jigawa Sule Lamido

A yau Juma'a kuma ake sa ran zasu je birnin Yolan jihar Adamawa don mika goron gayyatar shiga jam'iyyar ta APC ga gwamnan Jihar.

Sai dai wasu daga cikin gwamnonin sabuwar PDP sun ce za su yi shawara tukunna.

Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa duk matakin da zai dauka, sai ya tuntubi jama'arsa tukuna.

'APC bata da akida da manufofi na hakika'

Jami'yyar PDP mai mulki a Najeriya ta bayyana sabuwar gamayyar jam'iyyun adawar ta APC a zaman jam'iyyar munafukai wacce ba ta da akida da manufofi na hakika.

A cikin wata sanarwa da ta aikewa kafafen watsa labarai, jam'iyyar ta PDP ta ce irin yadda APC take zawarcin wasu gwamnoninta, ya nuna karara cewar APC ba ta da jama'a da kuma 'yan takara da ka iya cin zabe, har sai ta shiga gandun PDP ta yiwo farauta.

Sanarwar ta kara da cewa babu wani dan PDP na gaske da zai bar jam'iyyar ya koma APC.

Karin bayani