An takaita shan Sigari a NewYork

Taba Sigari
Image caption An kada kuri'ar da zata takaita shan Taba

Majalisar birnin New York a Amurka ta kara tsaurara matakan hana matasa sayen taba sigari da dangogin sa.

An kada kuri'a dan kara adadin shekarun wadanda za su iya sayar taba sigarin daga shekaru sha takwas zuwa ashirin da ya.

Wannan zai sa birnin New york zama na farko da ya kafa doka irin wannan a fadin Amurka.

Magajin garin Michael Bloomberg wanda yake jagorantar yaki da shan taba sigari ya ce haram ta shan tabar zai taimaka wajen rage yawan kananan yaran da suke shan ta.

Kashi takwas cikin dari na masu shan sigari a New york sun fara wannan dabi'a ne kafin su kai shekaru ashirin da ya.

Karin bayani