'Yan Nijar 92 sun mutu a cikin hamada

Image caption Akwai dubban jama'a dake ketarawa zuwa Algeria daga Niger

Gwamnan jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar, ya ce an gano gawarwakin mutane 92 a cikin hamada bayan da motar dake dauke dasu ta lalace a kan hanyar zuwa Algeria.

Kanar Garba Makido ya ce mutanen da suka hada da mata da maza da kuma kananan yara, sun mutu ne sakamakon kishirwa.

Hukumomi sun ce wata mata daga cikin mutane 21 da suka tsira, ta lallaba ta taka zuwa birnin Arlit inda ta nemi agaji.

'Rubabbun gawarwaki'

Wani jami'in ceto Almoustapha Alhassan ya ce gawarwakin sun rube yayin da namun daji su ka cinye wasu sassansu.

Ya kara da cewar " wasu daga cikin yaran da suka mutu na rike da alluna da kuma Alkur'ani mai tsarki.

Adadin gawarwakin da aka gano a yankin cikin makon guda yanzu ya kai 113.

Babu tabbas ko 'yan ci-ranin na kan hanyarsu ne ta zuwa Turai ko kuma Algeria mai makwabtaka da Nijar.

Karin bayani