An gano gawarwakin 'yan ci-rani 87 a Nijar

Hamadar Sahara
Image caption Hamadar Sahara

Masu aikin ceto a Nijar sun gano gawarwakin mutane 87, 'yan ci-rani, da kishirwa ta kashe su bayan motarsu ta lalace lokacin da suke kokarin ketara Sahara.

Mafi yawansu dai mata ne da kananan yara.

Wani jami'in ceto Almoustapha Alhacen yace gawarwakin sun rube yayin da namun daji su ka cinye wasu sassansu.

Adadin gawarwakin da aka gano a yankin cikin makon guda yanzu ya kai 113.

Babu tabbas ko 'yan ci-ranin na kan hanyarsu ne ta zuwa Turai ko kuma Algeria mai makwabtaka da Nijar.