Stella Oduah ta bayyana a gaban majalisa

stella oduah
Image caption stella oduah

Ministar kula da sufurin jiragen sama a Najeriya, Stella Oduah ta musanta cewa ta sabawa doka a batun sayen wasu motoci biyu masu sulke kan kudi naira miliyan 255.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nigeria ce dai ta sayi wadannan motoci domin amfanin ministar.

Stella Oduah ta bayyana haka ne lokacin da ta gurfana a gaban wani kwamitin da majalisar wakilai ta kafa domin bincikar batun sayen motocin.

Ranar Laraba ne dai ya kamata ministar ta bayyana a gaban kwamitin, amma bata yi ba, abun da yasa kwamitin ya yi barazanar aika mata da sammacin kama ta.

Stella Oduah ta ce lallai ta samu amincewar majalisar kafin sayen motocin, batun da 'yan majalisar suka musanta. Kuma ta rubuta wa hukumar kula da sufurin jiragen sama da su bi duk wata ka'ida wurin sayen motocin.

Dangane da haka ne sauran manyan jami'an ma'aikatar da suka bayyana gaban kwamitin su ma su ka yi kokarin kare kansu.

Sai dai 'yan majalisar sun nuna rashin gamsuwa da bayanin ministar, inda suka ce a matsayinta na babba ita ce ya kamata ta tabbatar na kasanta sun yi aiki bisa doka.

Wakilin BBC yace abinda ya rage wa kwamitin shi ne tattara bayanan da suka samu tare da hada rahoton da zasu mikawa zauren majalisar.