'Ana tilastawa 'yan gudun hijirar Syria komawa Kasar su'

Syria_Jordan
Image caption 'Yan gudun hijira fiye da miliyan biyu be suka tsere daga Syria

Sabon rahoton da kungiyar kare hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta fitar ya ce ana maida daruruwan mutanen da ke gujewa rikicin Syria a iyakar kasar da Jordan da wasu kasashe masu makwaftaka.

Rahotan ya ce mutanen da ake hanawa shiga kasashen sun hada da Palasdinawa da 'yan gudun hijirar Iraqi wadanda suke zaune a Syriar, da wadanda ba su da takardun shaida da kuma mazan da basu da iyali a Jordan.

Amnesty International ta ce ba za a yadda da hakan ba.

Sai dai hukumomin Jordan sun ce sun bar iyakokin kasar su a bude ga 'yan gudun hijirar Syriar.

Karin bayani