An yi sabon artabu a Tripoli na Libya

Masu zanga zanga na Libya

An bayar da rahoton samun sabon artabu a Tripoli babban birnin Libya, kwana daya bayan kashe mutane da yawa ko kuma jikkata wasu a lokacin wata zanga zangar kin jinin sojin sa kai.

Ana tashin hankalin ne a wajen gabacin birnin Tripolin tsakanin sojin sa kai na yankin da kuma mayakan da suka je daga birnin Misrata. Tashin hankalin na jiya ya hada da sojin sa kan Misrata wadanda suka bude wuta a kan masu zanga zangar dake neman sai sun bar Tripolin.

Ma'aikatar kiyon lafiya ta ce mutane 43 ne aka kashe sannan wasu 500 suka samu raunuka a rikicin wanda a cikinsa masu zanga zanga suka kaddamar da harin ramuwar gayya a kan sojin sa kan.

Pirayim Minista Ali zeidan ya bukaci dukanin bangarorin da su nuna juriya sosai.