Isra'ila ta kai wa Syria hari

Jirgin Yaki
Image caption Israila ta kai harin kusa da garin Latakia na kasar Syria da ke gabar teku

Wasu jami'an gwamnatin Amurka sun ce jiragen yakin Israela sun kaddamar da wasu hare-hare a kusa da garin Latakia na kasar Syria da ke gabar teku.

Wani jami'in gwamnatin Amurka da bai so a ambaci sunansa ba,ya ce an kai harin ne kan wasu makamai masu linzami kirar Rasha da ake shirin mika wa kungiyar Hezbolla da ke kasar Lebanoon.

Sai dai jami'an Israela sun ki cewa uffan game da zargin,haka kuma ba a iya tantance ainahin lokacin da a ka kai harin ba.

Wannan harin ya zo ne a wani lokaci da ake bukatar taka tsan-tsan, yayin da Rasha da Amurka ke kokarin shirya wani taro kan samar da zaman lafiya a Syria.

Karin bayani