Google ya fitar da wayar 'Nexus 5'

Image caption Nexus 5

Kamfanin Google ya kaddamar da sabuwar wayar komai da ruwanka mai suna Nexus 5.

Wayar Nexus 5 wacce kamfanin LG ya kerawa google, ta fi wayar Nexus 4 kankanta, da rashin nauyi sannan kuma fuskarta nada fadi sosai.

Google da LG sun kulla kawance don yin kasayya da kamfanonin Samsung da kuma Apple.

Amma duk da haka wayoyin iphone dana Samsumg sun fi wayoyin LG farin jini a duniya.

An soma sayar da sabuwar wayar Nexus 5 wacce aka yiwa lakabi da 'kitkat' a ranar 1 ga watan Nuwamba a kasashen Amurka, Birtaniya, Canada, Australia, France, Jamus, Spain, Italiya, Japan da kuma Koriya.

A Birtaniya za a sayar da wayar a kan fan 299 amma a Amurka ana sayar da wayar a kan dala 349.

Karin bayani