Zaman dar-dar bayan kisan Hakimullah

Hakimullah Mehsud
Image caption Hakimullah Mehsud

An tsaurara matakan tsaro a Islamabad babban birnin Pakistan da sauran yankunan kasar, bayan kisan shugaban Taliban Hakimullah Mehsud.

A jiya ne a ka hallaka shi tare da wasu mutanen a harin da a ka kai masa a yankin arewacin Waziristan.

A yanzu ana fargabar irin martanin da 'yan Taliban din za su mayar.

Wani jirgin da bai da matuki ne ya kai hari a gidan da Hakimullah Mehsud ke zaune kwana daya kamin ziyarar da tawagar masu sasantawa daga Islamabad za ta kai masa.

Shi da wasu manyan shugabannin Taliban, domin yi masu tayin shiga tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin Pakistan.

A cewar wani babban minista a gwamnatin, an yi wa shirye-shiryen gwamnati karan tsaye.

Ko da yake sauran jami'ai sun ce, ba zasu yi watsi da abin da suke ganin wani muhimmin bangare ne na manufar Praminista Nawaz Shariff dangane da tabbatar da tsaro ba.

Rahotanni sun ce, manyan shugabannin Taliban suna ganawa yau a arewacin Waziristan domin zaben sabon shugaba.

kuma zaben na iya daukar kwanaki da dama.

Kisan Hakimullah Mehsud wani babban koma baya ne ga kungiyar Taliban, bayan da a farkon wannan shekarar aka hallaka mataimakinsa.

Sannan kuma dakarun Amirka suka kama daya daga cikin na kurkusa da shi a Afghanistan.