Amirka na son demokradiyya a Masar

John Kerry
Image caption John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce Amirka ta sha alwashin yin aiki tare da gwamnatin rikon Masar domin maido da demokradiyya a kasar.

Ya fadi hakan ne ganawar da yayi a birnin Alkahira tare da hukumomin Masar din, wadanda sojoji ke mara wa baya.

John Kerry ya bayyana Masar a matsayin abokiyar kawancen Amirka, yana mai cewa cigaban kasar ta fannin siyasa dana tattalin arziki suna da matukar muhimmanci ga yankin baki daya.

Ya kuma sassauta kalamai akan jingine tallafin da Amirka ke baiwa Masar din ta fannin soji, bayan da aka kawar da shugaba Mohammed Morsi a watan Yuli, yana mai cewa dokokin Amirka ne suka tanadi hakan.

Wata jarida a kasar ta Masar ta wallafa hotunan tsohon shugaba Mohammed Morsi, wadanda ta ce sune na farko tun bayan da aka tsare shi.

Sai dai ba wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.