An kashe 'yan jaridu biyu a Mali

Image caption An kashe 'yan jaridar RFI biyu a Mali

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da cewa an kashe 'yan jarida biyu dake aiki da gidan radiyon Faransa watau RFI a arewacin Mali.

A cikin wata sanarwa ma'aikatar ta ce an ga gawar Ghislaine Dupont da ta Claude Verlon bayan da tun farko wasu 'yan bindiga suka sace su a garin Kidal.

Wani kakakin gwamnatin Mali Mahamane Baby ya karanta wata sanarwa wadda ke nuna juyayin gwamnati game da kisan.

Mahamane Baby yace, "gwamnatin kasar Mali ta ji takaicin sacewa da kisan wasu 'yan jarida biyu na RFI a ranar assabar a Kidal.

Shugaba Francois Hollande ya bayyana takaicinsa ga abinda ya bayyana a matsayin wata halayya ta mugunta.

'Yan bindigar sun tilastawa 'yan jaridun biyu shiga wata budaddiyar mota inda suka ruga da su cikin hamada.

Karin bayani