An kashe mutane a turmutsitsi a Cocin Najeriya

Image caption turmutsitsi ya kashe mutane sama da ashirin a Najeriya

Mutane a kalla ashirin da takwas ne aka kashe a Najeriya a wani turmutsitsin da ya biyo bayan wata addu'ar tsakiyar dare da aka yi a wani Coci a Jihar Anambra.

A turmutsitsin dai an raunata wasu mutane da dama.

Har yanzu dai ba a tantance abinda ya haddasa turmutsitsin ba a cikin daren jiya a Cocin Nkapor dake jihar Anambra.

Gwamnan jihar, Peter Obi wanda ya halarci addu'ar da aka yi don zagayowar ranar All Saints Day ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike.

Karin bayani