Sulhun Pakistan da Taliban na tangal-tangal

Image caption Pakistan na ganin Amurka tayi mata zagon kasa

Pakistan ta zargi Amurka da yi mata zagon-kasa da gangan a yunkurin da take yi na farfado da tattaunawar sulhu bayan da Amurkar ta hallaka Hakimullah babban kwamandan Taliban din a wani harin jirgi maras matuki.

Ministan cikin gidan kasar Chaudry Nasir Ali Khan ya ce mutuwar Hakimullah Mehsud itace mutuwar dukkan wani kokari na samun zaman lafiya da 'yan gwagwarmayar.

Nasri Ali Khan ya ce, "Gwamnatin Pakistan, ba wai tana kallon wannan harin ba ne a matsayin hari a kan wani mutum, tana kallonsa ne a matsayin hari a kan dukkan shirin neman zaman lafiya."

Jami'ai a birnin Islamabad sun kira Jakadan Amurka dake kasar, Richard Olson ya ba da bahasi kan wannan harin na Amurka.

Ma'aikatar harkokin waje a birnin Washington na Amurkar dai ta ki cewa uffan kan wannan sukar da Pakistan ke yi, amma daga bisani a wata sanarwa ta bayyana cewa kisan na Hakimullah ya biyo bayan hannun da yake da shi ne a hare-haren da ake kai wa Amurkawa da bukatun ta.

Karin bayani