An caji wanda ya kai hari a Los Angeles

An kai hari a filin jirgi na Los Angeles
Image caption An caji wanda ya kai hari filin jirgin saman Los Angeles na Amurka

Masu gabatar da kara a kasar Amurka sun gabatar da cajin kisan kai ga dan bindiga dadin nan da ake zargin ya kai hari a filin jirgin sama na Los Angeles.

An kashe jami'in tsaro daya a harin tare da raunata wasu mutanen biyar da suka hada da jami'an tsaro.

Mutumin da ake zargi Paul Ciancia dan shekaru 23 da haihuwa - shi kansa an yi masa rauni aka kuma yi awon gaba da shi.

Jami'ai sun ce an samu wata takarda cikin jikkarsa inda ya rubuta cewar ya shirya kashe jami'i daya ko fiye da haka cikin ma'aikatan na hukumar tsaro ta sufuri.