An hallaka 'yan biki a jahar Borno

Jahar Borno a taswirar Najeriya
Image caption Jahar Borno a taswirar Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun hallaka akalla mutane 30 bayan da suka kai hari kan wani ayarin motocin daurin aure a jahar Borno.

Wasu rahotanni sun ce daga cikin wadanda aka kashen har da angon.

Harin ya auku ne a jiya Asabar a kauyen Firgi dake tsakanin garin Bama zuwa Gwoza, lokacin da 'yan bikin ke komawa jihar Borno daga Adamawa inda aka yi daurin auren.

Ana dai zargin 'yayan kungiyar Boko Haram da kai wannan hari.

Shaidu sun ce sun ga gawarwaki barjak a bakin hanya, yawancinsu da harbin bindiga.

A watan Mayun da ya wuce ne aka kafa dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

An kuma tura karin sojoji domin murkushe masu fafutukar na Boko Haram.