Ana ci gaba da gumurzu a Congo

'Yan tawayen M23
Image caption 'Yan tawayen M23

Dakarun sojin jamhuriyar demokradiyyar Congo--- tare da goyan bayan dakarun Majalisar Dinkin Duniya--- sun kara zafafa bude wuta a wuraran da har yanzu 'yan tawayen M23 ke da karfi.

Sojojin sun ce sun gama da garin Mbuzi, daya daga cikin garuruwa uku da skai saura a hannun 'yan tawayen.

Yayin da dakarun Majalisar Dinkin Duniya ke ta ruwan harsasai a sauran garuruwan biyu.

Jiragen helkwaptan Majalisar Dinkin Duniya na ta yin ruwan bama-bamai a garin Chinzu, inda nanan ne aka ce yawancin manyan kwamandojin M23 din suke.

'Yan tawayen sun maida martani a garin Bunagana, inda suka kashe akalla mutane hudu.

Yanzu haka dubban 'yan gudun hijira ne suka tsere zuwa Uganda.