Korea ta kudu da Japan sun sami baraka

Image caption An sami baraka tsakani Korea ta Kudu da Japan

Shugabar Korea ta Kudu ta nuna babbar barakar da aka samu a dangantakar kasar da Japan.

Wannan na zuwa ne a yayinda yankin ke gwagwarmayar ceto kansa daga kwarewar da Korea ta Arewa ke kara samu ta fuskar nukiliya.

Lokacin da take magana da BBC Shugaba Park Guyen ta ce ita ba ta ga wani amfanin dake tattare da yin wani taron koli da Pirai Ministan Japan Shinzo Abe ba, sai fa idan kasar ta nemi afuwa ga rashin mutuncin da ta aikata a lokacin yaki.

Wakilin BBC a Japan ya ce, a yanzu ana tababa kan yarjejeniyar da kasashen biyu za su rattaba hannu kan ta, ta musayar bayanai na leken asiri.

Karin bayani