Cuta ta bulla a Tillabery na Niger

Image caption Shugaban Nijar, Muhammadou Issoufou

Hukumomin kiwon lafiyar a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da bullar wata sabuwar cuta a cikin jahar Tillabery da ya zuwa yanzu likitoci ba su kai ga tantance ko wace iri ce ba.

Alamomin cutar sun hada da zazzabi da amai da kuma zubar jini ta hanci da baki.

Kawo yanzu mutane bakwai sun rasu daga cikin fiye da ashirin da suka kamu da cutar.

Ma'aikatar lafiya ta Nijar da taimakon hukumar lafiya ta duniya, WHO na ci gaba da bincike don gano musababbin cutar.

Karin bayani