'Yan ci-rani sun sha da kyar a Nijar

Hanyar da 'yan ci-rani ke bi
Image caption Hanyar da 'yan ci-rani ke bi

A Nijar hukumomin jahar Agadez sun gano wasu 'yan ci-rani fiye da saba'in, mata da kananan yara, wadanda suka rasa na yi a cikin hamada bayan motar da ta dauko su daga Algeria zuwa Nijar din ta lalace.

Tuni dai aka mika su hannun kungiyar kula da 'yan ci-rani ta IMO ko OIM domin duba yadda za a yi a kai su garuruwansu.

An ce mutanen 'yan asalin yankin Matameye ne a jahar Damagaram.

Tawagar gwamnan jahar Agadez ce da ta je yin addu'o'i a kusheyin mutanen da suka hallaka ta yi kicibis da 'yan ci-ranin, sun rasa na yi bayan motar da ta dauko su daga Tamanrasset a Algeria ta yi faci.

A makon da ya gabata ne dai aka gano gawarwakin wasu 'yan ci ranin 92, galibinsu mata da kananan yara, wadanda kishirwa ta hallaka yayin da suke kokarin zuwa Algeriar.

A karshen mako kuma hukumomin na Nijar suka farauto wasu 'yan ci ranin fiye da dari wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa Algeria.