Goodluck Jonathan ya gana da ASUU

Image caption Jonathan ya shafe sa'o'i 13 yana ganawa da ASUU

A Najeriya, shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya gana da shugabannin kungiyar malaman jami'o'in kasar da nufin kawo karshen yajin aikin da suke yi.

Shugaba Jonathan dai ya shafe sa'oi kusan goma sha uku yana tattaunawa da Malaman Jami'ar.

Sai dai duka bangarori biyun ba su yi wani cikakken bayani a kan abin da suka cimma a zaman ba.

Kodayake bangaren gwamnatin tarayya ya ce ana gab da shawo kan matsalar.

Su kuwa masu wakiltar malaman Jami'ar sun ce sai sun zauna da Kungiyar kafin su fitar da matsaya.

Dalibai dai a Najeriya dake karatu a Jami'oin kasar na damuwa da tsawon yajin aikin da ya kai kusan watanni hudu ana yi.

Karin bayani