UN: Boko Haram na aikata laifukan yaki

Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce Boko Haram matsoraciya ce

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mai yiwuwa a sanya kungiyar Boko Haram a cikin kungiyoyin da ke aikata laifukan yaki.

Kakakin hukumar, Cecile Pouilly, ta ce "idan aka hakkake cewa mambobin kungiyar Boko Haram da takwarorinta sune ke kai hare-haren da ake kai wa fararen hula, hakan zai zama laifin cin zarafin bil Adama.''

Hukumar ta kuma yi Alla-wadai da harin da 'yan kungiyar suka kai wa wasu mutane da ke kan hanyarsu ta dawowa daga wajen daurin aure a jihar Borno da ke Nigeria.

Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Pouilly ta kara da cewa hare-haren da Boko Haram ke kai wa fararen hula da 'yan siyasa da ma'aikatan kasashen waje da makamantansu sun nuna cewa kungiyar matsoraciya ce.

A baya bayan nan dai 'yan kungiyar sun kai wani harin a kan babura da motocin a-kori-kura, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka mutane da dama.

Karin bayani