Sojojin Congo na gab da murkushe 'yan tawaye

Dakarun gwamnatin Congo
Image caption Dakarun gwamnati na kara dannawa yankunan 'yan tawaye

Sojojin gwamnati a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo wadanda dakarun Majalisar Dinkin Duniya ke rufa wa baya suna kara dannawa suna kwato sauran muhimman yankunan dake hannun 'yan tawayen kungiyar M23.

A yayin da ake cigaba da gwabza fadan, Shugabannin Afrika na yankin sun fara wata tattaunawa a kasar Afrika ta Kudu game da tashe-tashen hankulan dake faruwa da nufin hana sake afkuwar duk wani tawaye a gabashin Congo.

Rundunar Sojin ta Congo ta ce ta kwato daya daga cikin yankuna uku da 'yan tawayen suka kafa sansanoni.

Har ila yau kuma dakarun Majalisar Dinkin Duniya na cigaba da barin wuta a kan sauran yankunan biyu.

Fadan dai ya tilastawa dubban 'yan gudun hijira tserewa zuwa kasar Uganda.

Kwamishinan lardin Kisoro a kasar ta Uganda Ahmed Mustapha Doka ya shaidawa BBC cewar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo tana da sojoji a yankin tsakanin Uganda da kasar, wannan kuma shi ya sa fadan zai kara bazuwa kasar ta Uganda

Karin bayani