Majalisar Nigeria za ta binciki 'yan sanda

MD Abubakar, Shugaban 'Yan Sandan Najeriya
Image caption Wasu 'yan majalisar wakilai sun yi tur da kusten da akai wa Gwamonin 7

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci kwamitin ta mai kula da harkokin 'Yan Sanda da ya gayyaci Shugaban 'Yan Sandan Najeriya MD Abubakar domin yazo ya yi bayanin kutsen da ''Yan Sanda suka yi a taron Gwamnoni bakwai na PDP sabuwa da aka gudanar ranar Lahadi a gidan gwamnatin jihar Kano dake Abuja.

Ana sa ran kwamitin zai gabatarwa da majalisar wakilan rahotansa cikin makonni biyu.

Wasu 'yan Majalisar wakilan Najeriyar ne dai suka gabatar da wannan koke a zaman majalisar, inda su ka yi zargin abinda 'yan sandan suka yi, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

A ranar Lahadin data gabata ne dai wani babban jami'in 'Yan Sanda na gundumar Asokoro ya kutsa kai inda gwamnonin bakwai suke taro, bisa umarnin da ya ce an bashi daga sama.

Wannan lamari dai ya tada hayaniya a wajen da Gwamnonin suke taron.

Gwamnonin dai sun yi ikirarin cewa suna gudanar da taron ne a kokarin da ake na dinke barakar da ta kunno kai cikin jam'iyyar ta PDP.