Hukumomin Nijar sun ceto mutane 70 a Sahara

Image caption Ci rani a yankin Sahara na jefa mutane cikin hadari

A Jamhuriyyar Nijar, hukumomi a jihar Agadez sun gano wasu 'yan ci-rani fiye da saba'in, mata da kananan yara, wadanda suka rasa na yi a cikin hamada, bayan motar da ta dauko su daga Algeria zuwa Nijar din ta lalace.

A makon da ya gabata ne dai aka gano gawarwakin wasu 'yan ci ranin 92, galibinsu mata da kananan yara, wadanda kishirwa ta hallaka yayinda suke kokarin zuwa Algeriya.

Hukumomi a Jamhuriyyar Nijar din sun dauki matakin rusa sansanonin 'yan ci rani a Agadez.

Haka kuma hukumomin sun ci alwashin hukunta masu safarar mutane a kasar don gujewa asarar rayuka da ake yi ta wannan hanya.

Karin bayani