Saudiyya ta fara kamen Tukari

Image caption 'Yan ci-rani na fuskantar matsin lamba

Hukomomi a kasar Saudiyya sun fara daukar mataki a kan bakin haure dake kasar bayan wa'adin da aka debarwa 'yan ciranin dake aiki a kasar domin su gyara takardunsu ya cika.

Ranar Lahadi ne dai waa'din watanni shida ya cika da kasar ta ba wa duk mai zama kasar ya gyara takardarsa.

Hukumomin sun bada zabi ga 'yan ci rani ko su gyara takardunsu ko kuma su mika wuya a tusa keyarsu zuwa kasarsu ko kuma su fuskanci hukunci.

Wasu 'yan cirani sun ce lamarin ya jefa bakin haure da aka fi sani da suna Tukari cikin mawuyacin hali.

Karin bayani