An soma shari'ar masu kishin Islama a UAE

Image caption Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan

An soma tuhumar wasu 'yan kishin Islama 30 a wata kotu a Hadaddiyar Daular Larabawa-UAE bisa zargin kafa reshen kungiyar 'Yan Uwa Musulmi.

Mutanen wadanda Misrawa 20 ne da 'yan kasarta Hadaddiyar Daular Larabawa su 10 ana zarginsu da satar bayanai daga hukumar leken asirin kasar da kuma karbar gudunmuwa ba tare da izini ba.

Wadanda ake zargin sun musanta tuhumar, kuma sun yi zargin cewar an azabtar dasu a lokacin da suke tsare.

A watan Yuli, an samu wasu masu kishin Islama su 69 da laifin kokarin kifar da gwamnatin siyasar kasar.

Kuma tuni kotun ta yankewa musu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kaso.

Karin bayani