APC na zawarcin Gwamna Wammako

Gwamna Aliyu Wammako
Image caption Gwamna Wammako ya ce bai yanke shawara ba tukuna, sai abin da mabiyansa suka ce.

Shugabannin sabuwar hadakar jam'iyyun adawa a Najeriya sun kai ziyara Sakkwato a ci gaba da zawarcin wasu gwamnonin jam'iyya mai mulki ta PDP da zimmar jawo ra'ayinsu zuwa cikin jam'iyyarsu ta APC.

A yayin ganawarsu 'yan adawar sun gayyaci gwamnan jahar ta Sakkwato Alhaji Aliyu Wamakko zuwa cikin jam'iyyar tasu domin kara musu karfi wajen tunkarar jam'iyyar PDP mai mulki a zaben shekara ta 2015.

Wadanda suka jagoraci tawagar babbar jam’iyyar adawar zuwa Sakkwato dai sun hada da Shugaban jam’iyyar Chief Bisi Akande da tsohon shugaban mulkin Sojin kasar Janar Muhammadu Buhari mai Ritaya da tsohon gwamnan jahar Legas Chief Bola Tinubu da kuma tsoho kakakin majalisar wakillai Aminu Bello Masari.

Gwamna Aliyu Magatakarda ya ce yayi farin cikin da karbar bakuncin tawagar ‘yan adawar, kuma ya ce ba zai bayyana ko zai sauya sheka ba ko kuma a’a har sai abin da mabiyansa suka ce.

Karin bayani