'Watakila an kashe Arafat da guba ne'

Image caption Margayi Yasser Arafat

Masana kimiyya a kasar Switzerland da suka yi gwaje-gwajen a gawar shugaban Palasdinawa, marigayi Yasser Arafat sun bayyana cewa mai yuwa an kashe shi ne da gubar polonium.

A wani rahoto da kafar yada labarai ta Aljazeera da jaridar Guardian suka wallafa, masa na kimiyyar sun ce akwai gubar polonium din a kasusuwan Mr Arafat wanda adadinsa ya linka yawan da ya kamata ace yana dashi akalla sau 18.

Matar marigayin Arafat, Suha, wadda aka baiwa takaddar rahotan ta ce wannan ya tabbatar da cewa kisan gilla ne aka yi masa.

Yasser Arafat ya rasu ne shekaru taran da suka wuce bayan wata 'yar gajeriyar rashin lafiyar da ba a gane ta ba.

A bara ne aka tono gawar Mr Arafat yayin da ake ta takaddama kan cewa an kashe shi ne da guba.

A ko da yaushe dai Isra'ila na musanta hannu a mutuwar ta sa.

Karin bayani