Man City ta lallasa CSKA 5-2

Manchester City
Image caption Manchester City

Kwallaye ukun da Alvaro Negredo ya jefa a ragar CSKA Moscow sun tabbatarwa da Manchester City damar shiga matakin sili-daya-kwale na gasar Zakarun Turai a karo na farko.

Sergio Aguero ne ya fara cin kwallaye, inda ya zuba biyu kuma ya baiwa Negredo kwallo ya ci, kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan nasarar da ta yi a karawarsu ta farko a Moscow, City ta san cewa za ta iya shiga cikin kungiyoyi 16 na karshe a gasar idan ta sake nasara kuma Viktoria Plzen ta kasa doke Bayern Munich mai rike da kambin gasar.

Duk da haka Seydou Doumbia ya zarewa CSKA kwallo guda kafin hutun rabin lokaci sannan ya kara guda bayan an dawo.