Al-Qaida ta yi ikirarin kashe 'yan Jaridar Faransa

Dan bindigar al-Qaeda
Image caption An kashe Faransawan biyu a lokacin da suke bakin aiki.

Kamfanin dillacin labaru na Mauritania Sahara Medias yace ya samu wani ikirari daga 'yan bindigar dake da alaka da kungiyar al-Qaida a yankin Magrib cewa su ke da alhakin kashe 'yan jaridar nan biyu na Kasar Faransa a arewacin Mali a ranar Asabar din da ta gabata.

Ghislaine Dupont da kuma Claude Verlon na yiwa gidan Rediyon Faransa wani aiki ne a garin Kidal a lokacin da wasu 'yan bindiga suka sace su sannan suka harbe su har lahira.

Sanarwar da 'yan bindigar wadanda keda alaka da Al- qaida suka aike, tace an kashe 'yan jaridar biyu ne saboda yakin da sojojin Faransa suka jagoranta a arewacin Mali.

Sanarwar tace sojojin Faransan da na aikin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya na aikata miyagun laifuka a kullum akan al'ummar Mali da kuma Musulmi a arewacin yankin.

Karin bayani