Huawei zai samar da intanet samfurin 5G

Image caption Kamfanin Huawei a China

Kamfanin Huawei Technologies na China ya ce zai kashe akalla dala miliyan 600 wajen bincike a kan samar da intanet mai karfin 5G.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ta ce za su yi aiki a kan kara karfin intanet din daga matakin 4G zuwa 5G cikin shekaru hudu masu zuwa.

Shugaban gudanarwar kamfanin, Eric Hu ya ce zasu kara karfin intanet din ne domin biyan bukatun masu hulda dasu.

Intanet mai karfin 5G ya nunka 4G sau 100 wajen shiga yanar gizo.