An haramta acaba a Monrovia

Image caption 'Yan Acaba a Monrovia

An haramta acaba a birnin Monrovia na kasar Liberia, abinda ya tilastawa daruruwan mutane zuwa wuraren aiki a kafa.

'Yan sanda sun kafa shingaye a kan tituna don tabbatar da cewar babu dan acabar da ya taka dokar.

Ana zargin 'yan acaba da tukin ganganci da kuma janyo hadura a kan tituna.

A galibin biranen Afrika, ana amfani da achaba a matsayin hanyar sufuri, inda wasu daga cikin 'yan acaba kan dauki mutane hudu ko biyar a kan babur, a mai makon mutane biyu da doka da tsara.

Duk dan acabar da ya karya dokar a Monrovia zai biya tarar dala 200.

Wani dan acaba Daniel Howard, ya nuna rashin jin dadinsa game da dokar inda ya ce suna biyan haraji ga gwamnati kuma an tauye musu hakkinsu.

Karin bayani